
Gwamnatin Jihar Gombe, ta ceto yara 59 da ake zargin an yi safararsu cikin watanni takwas da suka gabata.
Daraktan Hukumar Sufuri na jihar Gombe, (Gombe Line) Dakta Sani Sabo, ya bayyana hakan, yana mai cewa sun samu nasarar ne sakamakon sabon tsarin sufuri da jihar ta kafa, wanda ya haɗa dukkanin tashoshin mota a waje ɗaya domin samun tsaro mai inganci.
“Haɗin gwiwar da ke tsakanin ‘Yansanda da hukumomin NDLEA da NAPTIP da NSCDC ya taimaka wajen daƙile manyan laifuka kamar safarar yara da miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
“Mun ceto yara 59 tare da kama miyagun ƙwayoyi da makamai,” in ji Dakta Sabo.
“Yanzu ana rubuta bayanan kowane fasinja da motar da zai hau ta hanyar tsarin rajista na tashar.” In ji shi.
Wasu direbobi sun bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen tabbatar da tsaro, ko da yake hakan na jinkirta tafiya.
Wasu kuma sun ce farashin sufuri ya ɗan ƙaru sakamakon sabon tsarin.
Mutane da ƙungiyoyin farar hula sun yaba da nasarar, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa yaran da aka ceto sun samu kulawa da ilimi da kuma sada su da iyayensu.