Gwamnatin Congo da ƴan tawayen M23 sun amince su ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya, bayan da Qatar ta shiga tsakani, yarjejeniyar wadda za’a rattaba mata hannu cikin wata mai zuwa.
Yarjejeniyar za ta ƙunshi tsagaita wuta na dindindin da kuma dawo da mutanen da suka ɗaiɗaita.
Sai dai babu haske kan ko mayaƙan M23 sun amince su miƙa wasu yankunan gabashin Congo da suka ƙwace ikonsu ga gwamnati.
Wakilin BBC ya ce mutane da dama suna neman sanin ko wannan yarjejeniya ta ƙarshe da ake sa ran za a rattaba hannu kan ta a cikin watan Agusta za ta yi tasiri.
Akwai kuma rahotannin ƙaruwar tashin hankali tsakanin ƙungiyoyi masu riƙe da makamai a yankin, lamarin da ya tilasta wa dubban mutane tserewa.
