Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin naɗe-naɗe da ƙarin girma ga wasu jami’an gwamnati, a wani yunkuri na ƙarfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a sassan jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.
Daga cikin waɗanda aka naɗa, akwai Abdulkadir Balarabe Kankarofi, wanda aka naɗa a matsayin Mai baiwa gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Jin-ƙai.
Haka kuma, an naɗa Hajiya Aisha Tamburawa a matsayin mai baiwa gwamnan Shawara kan yada manufofin gwamnati.
- Gwamnan Kano Ya Taya Premier Radio Murnar Cika Shekaru 4
- NNPP ta bayyana takaicinta kan ficewar gwamnan Kano daga jam’iyyar
Sai Injiniya Mukhtar Yusuf wanda aka ɗaga darajarsa sa ya zuwa Shugaban hukumar WRECA, yayin da Zakari Usman Balan aka naɗa shi a matsayin mataimakin sa.
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Dr Mukhtar Bello Maisudan a matsayin Babban Sakataren Hukumar bada tallafin Karatu ta Kano.
Haka zalika, Injiniya Abba Kankarofi ya zama Shugaban Hukumar gyara da Kula da Hanyoyi ta Kano wato Karma.
Yayin da Musayyib Kawu Ungoggo aka naɗa shi a matsayin Shugaban hukumar gudanarwa Gidan Namun Daji na Kano.
Gwamna Abba ya bukaci sabbin jami’an da aka naɗa da waɗanda aka ƙarawa girma da su tabbatar da suyi aiki bisa jajircewa, gaskiya da kuma sadaukarwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jaddada cewa gwamnatin sa zata ci gaba da mayar da hankali kan ƙarfafa hukumomi da aiwatar da mulkin da ya shafi walwalar jama’a, bisa tsarin sabon shirin nan na Kano ce farko wato Kano first agenda.
