Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya gargadi yan siyasa game da sanya siyasa a harkokin tsaro, yana mai cewa hadin kai da zaman lafiya ga Najeriya Wajibi ne su kasance kafin muradun kashin kai ko na siyasa.
Da yake jawabi a lokacin da manyan jami’an Ma’aikatar Tsaro ta Jiha suka kai masa ziyara a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna Gwamna Uba Sani ya gargadi yan siyasa da su Daina sukar manufofin gwamnati da ayyukan da ka iya zama barazana ga hadin kan kasar.
Wasu muhimman abubuwa da Malamai suka tattauna a Kaduna
Waiwaye: Wasu manyan abubuwan da suka faru a jihar Kano a 2024
Maganar Kisan Gillar Kiristoci a Najeriya ba gaskiya bane – Jakadan Amurka
Gwamnan Ya yi Allah wadai da abin da ya kira munanan dabi’un wasu yan adawa wadanda ke bata sunan Najeriya don samun riba ta siyasa yana mai bayyana irin wadannan ayyuka a matsayin rashin kishin kasa da kuma barazana ga zaman lafiyar kasa.
Gwamna Sani ya tunatar da yan siyasa cewa mukaman siyasa na wucin gadi ne, amma Najeriya za ta ci gaba da kasancewa, yana gargadin manyan mutane game da amfani da addini da rashin tsaro don samun riba ta siyasa.
Gwamna ya bukaci yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa da kuma tallafawa kokarin da hukumomin tsaro ke yi don kare kasar.
Hassan Mamman Lagos, ya yaba wa Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa Malam Nuhu Ribadu, da Darakta Janar na hukumar tsaron Farin kaya ta DSS, Adeola Ajayi, saboda rawar da suka taka wajen magance kalubalen tsaro a fadin kasar.
