Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bukaci ɗaliban da suka kammala karatu a jami’o’in Najeriya da ƙasashen waje, da su yi amfani da takardun shaidar karatunsu wajen kirkire-kirkire, magance matsalolin al’umma da samar da damarmakin ayyukan yi, maimakon dogaro da neman aikin gwamnati ko na kamfani.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyu na jami’ar Baba Ahmed da ke unguwar Sharada, inda ya kuma ƙaddamar da wasu manyan ayyukan gine-gine guda uku da jami’ar ta gudanar.
Gwamna Yusuf ya ce ilimi shi ne ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa, kuma gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin samar wa matasa damar samun ingantaccen ilimi, domin su taka rawa wajen ci gaban al’umma.
Gwamnan ya ce matakan da gwamnatin sa ke ɗauka a fannin ilimi sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda Kano ta zama jiha mafi ƙwarewa a jarrabawar NECO har sau biyu a jere.
Gwamnan kuma yabawa wanda ya kafa jami’ar, Sanata Dr Yusuf Datti Ahmed, da shugabanta Farfesa Adamu Idris Tanko, bisa gudunmawarsu wajen bunƙasa ilimi.
