Gamayyar Kungiyoyin jihar Kano mai taken ONE KANO AGENDA ta bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf daya mayar da hankali wajen cigaba da ayyuka a fadin jihar.
Shugaban gamayyar Ambasada Abbas Abdullahi Yakasai ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta Kano.
Yakasai yace akwai bukatar gwamna Abba ya ci gaba da salon mulkin daya dauko na bunkasa Kano da ciyar da ita gaba, kar sauya shekar da yayi ta dauke hankalin sa ko canza masa tunani daga tsarin daya dakko.
Yakasai yace kafa majalisar dattawan Kano, da gwamna Abba Kabir Yusuf yayi zai taimaka wajen kawo hadin kai, zaman lafiya da girmama manya da Kuma kawo cigaban jihar.
Wakilin Kamal Umar Kurna ya rawaito mana cewar Kungiyar ta ONE KANO AGENDA tayi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf daya mayar da hankali wajen cigaba da aiyyuka domin amfanin al ummar Kano.
