Hukumomi a kasar Benin sun garkame akalla mutane 30 bisa zarginsu da hannu ga kokarin kifar da gwamnatin kasar da aka yi a farkon watannan.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito hukumomin na cewar an zargi mutanen ne da hadin baki da Sojin da su ka yi yunkurin kifar da gwamnatin.Idan ana iya tunawa a ranar 7 ga watan Disamban nan ne wasu Sojin kasar Benin suka bayyana a kafar Talabijin din kasar suka kuma yi jawabin kwace Iko daga hannun shugaban kasar Patricce Talon.
To sai dai wani agajin gaggawa da Sojin Najeriya suka kai wa Talon da kuma wasu kwararru daga kasar Faransa ya mai da wa Sojin hannun Agogo baya.
To sai dai kusan mutane 30 din da aka zarga duka sun bayyana gaban kuliya cikin tsauraran matakan tsaro, ana zarginsu da yaudara da kisa da kuma jefa tsarin tsaron kasar cikin rudani.
