Screenshot
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da tsayar da Mataimakin sa, Murtala Sule Garo, a matsayin abokin takararsa domin neman wa’adi na biyu a zaɓen gwamnan jihar da za’a gudanar a shekarar 2027.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da masu riƙe da muƙaman siyasa na gwamnatin tarayya daga jihar Kano, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon irin biyayya, jajircewa da kuma ƙwazon da Garo yake nunawa wajen ci gaban Kano tun bayan hawansu mulki.
Ya kuma yaba da kyakkyawar alaƙar aiki da ke tsakaninsu, yana mai cewa Murtala Garo ya nuna ƙwarewa, sadaukarwa da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na ya bayyana cikakkiyar amincewarsa da Mataimakin na sa, tare da kira ga shugabannin jam’iyya, masu riƙe da muƙaman siyasa da magoya baya da su ci gaba da haɗin kai domin ci gaba da nasarorin gwamnatin tare da shirin babban zaɓen shekarar 2027
