
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta fitar da gargaɗi mai zafi, tana kira ga ƙasashe da kada su kuskura su tsoma baki cikin rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ta hanyar amfani da ƙarfin soji.
Babban Sakataren MDD, António Guterres, ya bayyana damuwarsa da yuwuwar kara tsananta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai kira da a kauce wa duk wani “shiga tsakani na soji” da zai iya rura wutar rikicin da ke kara kamari.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta roƙi bangarorin biyu da su tabbatar da kare rayuka da haƙƙin fararen hula.
Babbar Sakatariyar ƙungiyar Agnes Callamard ta ce, wajibi ne Iran da Isra’ila su martaba dokokin haƙƙin bil’adama, domin kaucewa shan wahala ga waɗanda ba su da ruwa da tsaki a rikicin.