Hukumar shari’a ta jihar Kano ta ce za ta zauna da ’yan siyasar da ke amfani da shafukan sada zumunta wajen cin mutuncin juna da kalaman da ba su dace ba, domin shawo kan matsalar da kuma gyara tarbiyyar al’umma.
Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba ne ya bayyana hakan, yayin da yake tsokaci kan taron majalisar zartarwar hukumar, inda ya ce an amince da tattaunawa da ɓangarori daban-daban na al’umma domin magance matsalolin da ke kawo cikas ga zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa.
Sheikh DanAbba ya ce taron ya samu halartar wakilan ofishin Sakataren Gwamnatin Kano, Hukumar Hisbah da kuma Hukumar Zakka, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban al’ummar jihar.
A ƙarshe, Sheikh Ali Ɗanabba ya yi kira ga al’umma da su ƙara ƙaimi wajen sauke nauyin da ke kansu, domin tabbatar da kyakkyawar makoma.
