Hukumar Kula da kwashe shara da tsaftar muhalli ta Jihar Kano (REMASAB) ta kwashe tarin kayan gini da aka ajiye ba bisa ƙa’ida ba a kan Titin Guda Abdullahi da Titin Marhaba Cinema, da ke yankin Farm Centre a Kano.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Ahmad, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, Kwamitin Karta-Kwana na REMASAB ne ya gudanar da aikin a daren Laraba, 16 ga Satumba, 2026, biyo bayan koke-koken da wasu mazauna yankin suka shigar.
Manajan Daraktan REMASAB, Dr. Muhammad Salisu Khalil, ya ce hukumar ba za ta lamunci amfani da tituna wajen ajiye bulo, yashi, duwatsu da sauran kayan gini ba.
Ya bayyana cewa irin wannan dabi’a na iya haddasa haɗarin ababen hawa, cunkoso da kuma toshe magudanan ruwa.
Dr. Khalil ya ce hukumar za ta ɗauki duk kayan ginin da aka zuba a kan tituna ko wuraren da ba su dace ba a matsayin shara, tare da kwashe su.
Ya kuma yi kira ga masu ajiye kayan gini a kan tituna da su gaggauta kwashe su, yana mai gargadin cewa duk wanda ya ci gaba da karya dokokin muhalli zai fuskanci matakan da suka dace.
Hukumar ta kuma bukaci jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wuraren da ake zubar da kayan gini ko toshe tituna da magudanan ruwa.
