
Aminu Abdullahi Ibrahim
An koyar da daliban karamar sakandiren kimiya ta mai suna Injiniya Sagir Koki dake unguwar Tukuntawa sana’o’in dogaro dakai.
Cikin sana’o’in da aka koyar da daliban sun hada da hada abin markade da ake kira Blender da man shafawa da sabulun wanke-wake da sauran kayayyaki.
Matemakiya Shugabar makarantar Rimi City, Amina Farouk Abdullahi ce ta jagoranci horas daliban a wani yinkuri na tabbatar da cewa suna koyan sana’o’in da zasu dogara da kansu a nan gaba.

Ita shugabar makarantar karamar sakandiren ta Injiniya Sagir Koki, Hajiya Zaitun Abdullahi Mu’az, ta ce horas da daliban yayi daidai da tsarin manhajar koyar da dalibai.
Zaitun Abdullahi ta ce zasu cigaba da lalubo hanyoyin horas da dalibai sana’o’I daban daban.
