Rundunar ‘Yansandan Jihar Jigawa ta kama wata amarya bisa zargin saka guba wadda ta kai ga mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar 23 ga Janairun 2026, inda marigayin ya ci abincin rana da matarsa ta shirya masa a gida, bayan haka ya kamu da mummunar rashin lafiya.
- Kwankwaso Ya Yabawa ’Yan Sandan Kano Kan Cafke Masu Kisan Iyali a Dorayi
- ’Yan Sandan Kano sun ceto wanda aka yi Garkuwa da shi da kuma Naira Miliyan 4.85
An gaggauta kai shi asibiti domin samun kulawar likita, sai dai an tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa magani.
‘Yansandan sun ce an aika jami’ai nan take inda suka je suka kamo sabuwar amaryar wadda ita ake zargi.
A yayin da ake mata tambayoyi, amaryar ta bayyana cewa ta saka maganin ɓera a cikin abincin mijin nata, kamar yadda sanarwar ‘yansandan ta tabbatar.
Ta kuma bayyana cewa ta aiki ɗanuwanta ne domin sayo maganin ɓeran wanda ta yi amfani da shi wurin aikata laifin.
