Gwamnatin Jihar Kano ta gyara tashar tace ruwa ta Tudun Wada, inda aka dawo da samar da lita miliyan 2.2 na ruwa a kowace rana.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na farfaɗo da tashoshin samar da ruwan sha domin rage matsalar ƙarancin ruwa da al’ummomi ke fuskanta.
Ana sa ran gyaran tashar zai taimaka wajen inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga mazauna yankunan da take yi wa hidima.
Gwamnatin Kano dai na ci gaba da ayyukan gyara da inganta tashoshin ruwa daban-daban a jihar domin ƙara yawan ruwan da ake samarwa.
