Daga Ahmad Hamisu Gwale
Ana zargin barayi masu satar kayan lantarki ne suka sace kayayyakin wuta na wasu unguwanni a birni da suka hada da na fadar shugaban kasa watau Presidential Villa
Rahotanni sun bayyana cewa,wasu masu satar kayan wutar lantarki sun sanya fadar shugaban kasa da wasu unguwanni cikin duhu.
Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da Maitama, da Wuse, da Jabi, da Life Camp, da Asokoro, da Utako da kuma Mabushi.
Sai dai hukumar TCN mai raba wutar lantarki ta ce ta tura jami’anta domin yin gyara a inda aka sace kayan
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ndidi Mbah, ta ce wayoyin su ne ke kai lantarki ga cibiyoyin rarraba lantarki na kamfanin AEDC domin samar da lantarki ga al’umma.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce an lalata layin wutar lantarkinta na 132kV da wayoyin karkashin kasa wadanda ke kai lantarki zuwa cikin kwaryar Abuja da unguwannin da ke kewaye, lamarin da ya kawo katsewar lantarki.
Lamarin dai ya jefa unguwannin Abuja da dama cikin duhu, tare da haifar da wahalahalu ga al’umma.