Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, na binciken wasu gwamnoni 18 da ke kan mulki a yanzu.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ta bayyana haka, a wani taron wayar da kai da aka gudanar a Legas, wanda ya hada masu shirya fina-finai da yan canjin kudi domin tattauna matsalolin wulakanta takardun Naira da kuma lalata su.
Yayin amsa tambaya daga mahalarta taron, Olukoyede ya ce hukumar ba ta jiran sai shugabanni sun gama mulki kafin ta bincike su.
Ya ce a yanzu suna binciken gwamnoni 18 da ke kan mulki kuma sun fara binciken tun suna ofis saboda idan sun sauka sai su shiga mataki na gaba.Shugaban EFCC ya ce hukumar za ta ci gaba da aikinta ba tare da la’akari da matsayin mutum ba saboda almubazzaranci da rashin gaskiya da wasu shugabanni ke yi.
Kan wannan ikirari shugaban kungiyar yaki cin hanci da rashawa ta Transparency International a kasar nan, Auwal Musa Rafsanjani, ya yabawa kokarin hukumar sai dai ya ce katsalandin gwamnati na kawo cikas wajen daukar matakan da suka dace.
