Shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS sun hallara a birnin Abuja don buɗe babban taron ƙoli da za’a fara a yau Lahadi.
Taron na wannan lokaci zai fi mayar da hankali kan batutuwan tsaro.
Bayanai sun ce rashin tsaro da kuma juyin mulki – musamman masu sarƙaƙiya da aka samu a Guinea Bissau da kuma yunƙurinsa a jamhuriyar Benin – su ne batutuwan da za a fi mayar da hankali a yayin wannnan ganawa ta musamman.
Taron na zuwa ne mako guda bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Benin kan Shugaban kasar Patrice Talon, tare da damuwa kan rikicin siyasa a Guinea-Bissau da kuma taɓarɓarewar tsaro a Arewacin ƙasashen gabar tekun Yammacin Afrika.
Wannan shi ne taron ƙoli na farko da Shugaban kasar Sierra Leone Julius Maada Bio ke jagoranta a matsayin shugaban ECOWAS, inda ake sa ran zai jagoranci yanke muhimman shawarwari kan tsaron yankin.
Ana sa ran taron na Abuja zai kuma zama dandalin kammala bikin cika shekaru 50 da kafuwar ECOWAS, tare da yanke shawarwari kan matakan da ƙungiyar za ta ɗauka domin tunkarar ƙalubalen tsaro da siyasa da ke ƙara ƙamari a yankin yammacin Afrika.
