Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kalubalanci Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya fayyace matsayinsa na siyasa gabanin zaɓen 2027.
Lawal ya ce Wike ba zai iya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu ba, sannan a lokaci guda yana goyon bayan ƴan takarar wasu jam’iyyun siyasa a zaɓukan gwamnoni da na majalisu ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Television a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ke gudana a New York, inda ya ce Wike ya kamata ya bayyana a fili inda yake a siyasance.
Wike, wanda ke cikin jam’iyyar PDP, ya sha bayyana cewa zai mara wa Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, amma hakan ba zai hana PDP ko wasu jam’iyyun siyasa tsayar da ƴan takara a sauran zaɓukan ba.
Lawal ya kuma ce zai tattauna batun matsayar Wike da Shugaba Tinubu, yana mai cewa ya kamata a fayyace ko Wike yana cikin APC ko kuma ba ya cikinta.
Da yake mayar da martani kan sukar da Wike ya yi wa wasu gwamnonin APC, inda ya kira wasu “malalata”, Lawal ya ce Wike ya san waɗanda yake magana a kansu, sannan ya gayyaci masu son ganin ayyukan gwamnatinsa da su je Zamfara.
