Karamar Hukumar Bagwai ta yi rabon tallafin jarin Naira Dubu Hamsin-hamsin ga mata 100
An gudanar da bikin ne a sakatariyar karamar hukumar a ranar Talata, karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Bello Abdullahi Gadanya.
A jawabinsa a taron, shugaban Karamar Hukumar ya bayyana matukar godiyarsa ga gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusif bisa kudirinsa na tallafawa al’umma tare da inganta harkokin ci gaban mata.
Shugaban jam’iyar N N P P na Karamar Hukumar Alhaji Mas’ud Badau ya yi kira ga wadanda suka anfana da tallafin da su yi anfani da shi wajen inganta sana’oinsu domin dogaro da Kansu.
Daya daga cikin wadanda suka anfana da tallafin Malama Binta Hashim Jami’in a hirarta Kakakin Karamar Hukumar Shehu Bello Shanono, ta yi godiya ga gwamna da kuma shugaban karamar hukumar.
Ta kuma ce, jarin na zai taimaka mata matuka kuma hakan zai “habaka tattalin arzki da inganta zaman lafiya al’umma musamman ma a yankunan karkar”. Inji ta