
Aminu Abdullahi Ibrahim
Jami’an tsaro sun kama wani mutum mai suna Abulfatahi, wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin kasancewa ɗan leƙen asirin Boko Haram da kuma hannu a harin ta’addanci da aka kai a yankin Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Monguno a jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 27 ga Yuli, 2026, bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai bisa bayanan sirri domin tarwatsa wata ƙungiyar masu tattara bayanai da ke yi wa Boko Haram aiki a yankin.
Kafin hakan, an riga an kama wasu mutum biyu da ake zargin suna cikin wannan ƙungiyar, kuma an miƙa su cibiyar haɗin gwiwar tattara bayanan sirri domin ci gaba da bincike.
A yayin binciken farko, ana zargin Abulfatahi ya amsa cewa yana aiki ne ƙarƙashin wani kwamandan Boko Haram mai suna Akilu, wanda ake zargin yana jagorantar ayyukan ƙungiyar a yankunan Dabar Masara da Garin Mace.
Haka kuma ana zargin ya riƙa karɓar haraji a madadin ƙungiyar tare da taimakawa wajen zaɓen mutanen da ake sacewa a yankin Monguno.
Jami’an bincike sun kuma ce sun gano wasu lambobin waya guda biyu a wayarsa da ake zargin suna da alaƙa da kwamandan Boko Haram.
Ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin da kuma tarwatsa cibiyar da ake zargin tana taimaka wa ‘yan ta’adda.
