Kotun majistare da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, ta yanke wa wani matashi mai shekaru 26, Samuel Douglass, hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kwandunan tumatir guda hudu.
An gurfanar da Douglass a gaban kotun ne kan tuhumar satar tumatir da darajarsu ta kai naira dubu 140, wanda ake zargin ya aikata a watan Yulin 2026 a yankin Afunbiowo Estate da ke Akure.
Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa Douglass ya karɓi tumatirin ne daga wajen wanda yake masa aiki, Abimbola Akintomide, domin kai su ga wani direba a Ilesa Garage, amma a maimakon haka ya sayar da su tare da amfani da kudin.
Douglass ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, yayin da lauyansa ya roki kotun ta yi masa sassauci, yana mai bayyana shi a matsayin matashi kuma wanda bai taɓa aikata irin wannan laifi a baya ba.
A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Olusola Olujobi ta daure Douglass na tsawon watanni 12 tare da umartar sa da ya biya wanda aka yi wa laifin naira dubu 140, kotun ta ce idan ya gaza biyan kudin, zai ci gaba da zaman gidan yari na tsawon lokacin hukuncin.
