Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa binciken da ta kammala ya nuna cewa waɗannan hafsoshi sun aikata laifin yunƙurin kifar da gwamnatin.
Rahotanni sun bayyana cewa a watan Oktoban shekarar da ta gabata ne Hukumar Binciken Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta kama hafsoshi 16 masu muƙamai daga Kyaftin zuwa Birgediya-Janar, kan zargin yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu juyin mulki.
A ranar Litinin, kwamitin bincike da rundunar soji ta kafa ya kammala aikinsa tare da miƙa rahotonsa ga Shugaba Tinubu domin ɗaukar matakan da suka dace na gaba.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, Manjo-Janar Samaila Uba, ya tabbatar da cewa an miƙa rahoton kwamitin ga mahukuntan da suka dace.
A cikin wata sanarwa, Manjo-Janar Samaila Uba ya bayyana cewa za a gurfanar da duk waɗanda aka samu da laifi a gaban kotun soji, inda za a yanke musu hukuncin da dokokin aikin soji suka tanadar.
Ya ce sanar da jama’a halin da ake ciki na da nufin tabbatar da gaskiya da adalci, tare da nuna jajircewar rundunar soji wajen kiyaye ƙwarewa, bin ƙa’idoji, da kuma kare kundin tsarin mulkin ƙasa.
Rundunar Sojin Najeriya ta jaddada cewa za ta ci gaba da kasancewa mai biyayya ga dimokiraɗiyya, tare da kare tsaro da zaman lafiyar ƙasar.
