Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta sake tsare tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, jim kaɗan bayan an sako shi daga Gidan Yarin Kuje duk da cewa ya cika sharuddan belin da kotu ta gindaya masa.
Malami, wanda ya rike mukamin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a zamanin Tsohon Shugaban Kasa Muhammad Buhari, ya fito daga gidan yari ne bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa, inda a baya ta tsare shi kan zargin almundahanar kudade da Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa almundahana (EFCC) ke yi masa.
Tun da farko, kotun ta bayar da umarnin tsare Malami a Gidan Yarin Kuje bisa zargin safarar kudaden haram a lokacin da yake jagorantar Ma’aikatar Shari’a daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Gabanin bayar da belin, kotun ta tsare tsohon ministan tare da matarsa da dansa a gidan gyaran hali na Kuje daga watan Disambar 2025 zuwa farkon watan nan na Janairu 2026.
Daga bisani, Babbar Kotun Tarayya ta bayar da belin kowannensu a kan Naira miliyan 500, bayan da suka musanta dukkan zarge-zargen da EFCC ke yi musu.
