Shugaban Amurka Donald Trump ya fuskanci cece-kuce masu zafi bayan da ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Truth Social, wanda ya kunshi tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da matarsa Michelle Obama, a cikin wani yanayi da wasu suka bayyana a matsayin batanci da nuna wariya.
Bayan samun martani daga ‘yan siyasa daga bangarorin Democrat da Republican, Trump ya cire bidiyon daga shafinsa. Fadar White House ta bayyana cewa bidiyon “internet meme ne kawai” ma’ana abu ne na raha, ba a yi da wata manufa ba, kafin a cire shi gaba ɗaya.
Masu sharhi sun ce lamarin ya jawo muhawara mai zafi a Amurka, inda wasu ke ganin ya nuna kuskure daga bangaren Trump yayin da wasu ke kallon bidiyon a matsayin wani abu na nishadi na yanar gizo.
