Wata kotun tarayya a Amurka ta bayar da umarnin dawo da damar da kafafen yaɗa labarai na CNN, MS NOW da Politico ke da ita ta shiga Fadar Shugaban Ƙasa, bayan gwamnatin Shugaba Donald Trump ta hana su shiga harabar fadar.
Alƙalin kotun, Timothy Kelly, ya bayar da umarnin wucin gadi a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, yana mai cewa kafafen yaɗa labaran na da yiwuwar samun nasara a ƙarar da suka shigar kan matakin gwamnatin Trump.
Waɗannan kafafen yaɗa labarai sun shigar da ƙara ne bayan da gwamnatin Trump ta soke izinin shiga da ’yan jaridunsu ke da shi, bisa zargin cewa rahotanninsu na yaɗa labaran ƙarya da kuma bayanan da ba su dace ba. Sai dai kafafen sun ce matakin ya keta ’yancin aikin jarida da tanadin kundin tsarin mulkin Amurka.
A hukuncinsa, Alƙali Kelly ya ce akwai yiwuwar hana kafafen shiga fadar ya saba da tsarin shari’a, saboda ba a ba ’yan jaridun sanarwa a kan lokaci ko damar kalubalantar matakin ba. Ya kuma lura cewa wasu rahotannin da Fadar White House ta ambata a matsayin dalilin dakatarwar tsofaffi ne ko kuma rahotannin aikin jarida na yau da kullum.
Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na tsawon kwanaki 14 yayin da ƙarar kafafen yaɗa labaran ke ci gaba. Wannan hukunci ba shi ne ƙarshen shari’ar ba, amma ya tilasta wa gwamnatin Trump dawo da damar shiga Fadar White House ga CNN, MS NOW da Politico a yayin da ake ci gaba da sauraron ƙarar.
