Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Najeriya NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSCE ta shekarar 2026.
Hukumar ta ce ɗalibai 804,948, waɗanda ke wakiltar kashi 58.67 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar, sun samu maki biyar da suka haɗa da Darussan Turanci da Lissafi.
Magatakardar NECO, Dantani Wushishi, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Minna, babban birnin Jihar Neja.
A cewarsa, jimillar ɗalibai 1,378,048 ne suka yi rajistar jarabawar, yayin da 1,371,992 suka zauna rubuta jarabawar da aka gudanar daga ranar 15 ga Yuni zuwa 23 ga Yuli, 2026.
Wushishi ya ƙara da cewa ɗalibai 1,162,118, waɗanda ke wakiltar kashi 84.70 cikin 100, sun samu credit biyar ko fiye, ba tare da la’akari da sakamakonsu a darussan Turanci da Lissafi ba.
Ya ce adadin ɗaliban da suka samu credit biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi ya ragu da kashi 2.64 idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025.
A shekarar 2025, ɗalibai 818,492, wato kashi 60.26 cikin 100, suka samu credit biyar da suka suka samu irin wannan sakamako.
Haka kuma, Magatakardar ya bayyana cewa an samu raguwar yawan masu magudin jarabawa da kashi 64.74 cikin 100 a shekarar 2026.
Ya ce an gano ɗalibai 1,406 da ake zargi da aikata magudin jarabawa, adadin da ya ragu daga 3,878 da aka samu a shekarar 2025.
A ƙarshe, Wushishi ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sake naɗa shi domin wa’adi na biyu.
Ya kuma gode wa Ministan Ilimi, Tunji Alausa, bisa goyon baya da amincewar da ya nuna ga shugabancinsa.
