Ɗanwasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Dortmund da ke Jamus, Karim Adeyemi ya buɗe gidauniya a Najeriya.
Adeyemi, wanda yanzu yake wakiltar tawagar ƙasar Jamus, asalinsa ɗan Najeriya, kasancewar mahaifinsa ɗan Najeriya ne.
Ya buɗe gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke jiyar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya, inda ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi.
A kwanakin baya da ya ziyarci Najeriya, Adeyemi ya shaida wa BBC cewa nan gaba yana tunanin komawa taka leda a gasar Premier ta Ingila.
A gasar zakarun turai ta bana, ɗanwasan ya zura ƙwallo uku rigis a ragar ƙungiyar Celtic a wasan da suka fafata.
“Na san yadda rayuwa take a nan Najeriya da kuma yadda rayuwa take a Jamus.
Na daɗe ina da tunanin idan na samu ɗaukaka ta hanyar ƙwallon ƙafa, zan koma asalina a Najeriya in taimaka wa mutane. Ba zan taɓa mantawa da asalina ba. Wannan babban abin alfahari ne,” in ji shi.