Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da Naira dubu 20 ga ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi 44 dake jihar, domin tallafa musu gabanin bikin Eid in babbar sallah mai zuwa.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran ofishin Sakataren gwamnatin Kano Musa Tanko Muhammad ya fitar.
Sanarwar ta ce tallafin ya shafi ma’aikatan da ke matakan albashi daga na 01 zuwa 14 a ma’aikatun gwamnatin jihar da kuma kananan hukumomin.
Sanarwar ta rawaito cewa Matakin na zuwa ne bayan kammala biyan albashin watan Mayun shekarar 2026, kuma wani bangare ne na kokarin gwamnatin jihar na inganta walwala da jin dadin ma’aikata.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an dauki mataki ne la’akari da kalubalen tattalin arziki da karin bukatun da ke tattare da lokutan bukukuwa, domin baiwa ma’aikata damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala tare da iyalansu.
