Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun kama wani mutum ɗan ƙasar Sudan da ake zargi da kasancewa “mayaƙin ta’addanci ” na ƙasashen waje.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an kama mayaƙin ƙasar wajen ne a wani samame da dakarun suka kai a yankin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin yana da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, lamarin da ke nuna yiwuwar samun goyon baya daga wasu ‘yan ƙasashen waje ga ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Haka kuma rundunar ta ce sojojinta sun kama wata Mary Florence mai shekaru 36, wadda ta ce ‘yar ƙasar Ghana ce kuma ta shiga Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Rundunar ta ce tana binciken yadda ta isa yankin da kuma sahihancin bayanan da ta bayar game da asalinta da ayyukanta.
Rundunar ta bayyana cewa mutanen biyu suna tsare a hannun sojoji domin ci gaba da tantance su da gudanar da bincike kan yiwuwar alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci ko wasu hanyoyin aikata laifukan ƙetare.
