
Hukumar Yaki da Cutuka Masu Yaɗuwa Ta Ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa mutane 145 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a shekarar 2025, inda adadin mutuwar ya kai kashi 18.6 bisa ɗari na masu kamuwa da cutar.
Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da hukumar ta fitar a ƙarshen mako.
Hukumar ta kuma ce, an tabbatar da kamuwar mutane 781 da cutar daga cikin mutane 5,943 da aka yi wa gwaji a makonni 25 na shekarar nan.
Wannan alƙaluma ya nuna ƙaruwa da kashi 17.6 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Rahoton ya kara jaddada cewa kashi 91% na masu dauke da cutar sun fito ne daga jihohi guda biyar da suka haɗa da Ondo (31%), Bauchi (24%), Edo (17%), Taraba (16%), da Ebonyi (3%).
NCDC ta ce tana aiki tare da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar CDC ta Amurka da Cibiyar IHVN da kuma sauran hukumomin kula lafiya domin ƙarfafa matakan kariya da yaki da cutar Lassa a fadin ƙasar.