Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga shugaban Amurka Donald Trump, da ya mayar da hankali wajen tallafa wa Najeriya don ta yaki da matsalar tsaro, maimakon barazana ga ƙasar.
Tsohon shugaban mulkin sojan kasar, ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga shugaban kan zargin kisan gilla Kiristoci a saboda addininsu.
“Irin waɗannan kalamai na iya zama barazana ga ɗorewar haɗin kan Najeriya da ƙoƙarin da al’umma ke yi na tabbatar da zaman lafiya”. In ji shi.
Tsohon shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su hade kansu.
“Domin wannan lokaci ne da ya kamata mu haɗa kai a matsayin ‘yan ƙasa guda, mu kuma zuba hankali wajen kare martabar ƙasarmu, ba wai mu bari kalaman waje su raba mu ba.” in ji tsohon shugaban.
