
Ƙungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu da ta fara, inda ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.
Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai, a ranar Laraba.
“ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin bai wa gwamnati dama ta nuna kyakkyawan niyya wajen tattauna matsalolin da suka shafi albashi da kuma kayan aiki da inganta yanayin aiki a jami’o’in kasar”. In ji shi.
Ƙungiyar ta kuma ce, abin da ya sa suka janye yajin aikin shine gwamnati ta gabatar da matsayarta kan sabunta yarjejeniysar shekarar 2009 kuma da kiraye-kirayen da suka samu daga mutane da dama daga ƙasar domin sun janye yajin aikin.
Wannan ne ya sa ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.
Kungiyar ta kuma gargadi gwamnati da kada ta yi wasa da wannan lokaci, inda ta ce idan buƙatun nasu ba a warware su ba, za ta ɗauki mataki na gaba.