Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa yankuna 178 da ke cikin kananan hukumomi 28 na Jihar Kano na cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa a bana.
Shugabar hukumar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyan haka a yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki da kaddamar da Shirin Shirye-shiryen Tunkarar Ambaliya na Kasa na shekarar 2026 a nan Kano.
Zubaida Umar wadda daraktar hukumar mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma Aliyu shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta kasa (NiMet) da Hukumar Kula da Harkokin Ruwa suka yi ya nuna cewa wasu yankunan Kano na iya fuskantar ambaliya.
Aliyu Shehu ya ce NEMA ta gano kananan hukumomi 28 da ke cikin matsakaicin haɗarin ambaliya, a cikinsu akwai yankuna 178 da ke bukatar daukar matakan kariya na musamman.
Ya ce kananan hukumomin sun hada da Ajingi, Bagwai, Bebeji, Bichi, Bunkure, Dala, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Fagge, Gabasawa, Garun Mallam, Gaya, Gwale, Kabo, Karaye, Kiru, Kunchi, Ghari, Kura, Madobi, Rano, Rimin Gado, Sumaila, Takai, Tofa, Tudun Wada, Ungogo and Warawa.
Daga cikin al’ummomin da aka gano suna cikin haɗari akwai: Botangel, Komayu da Toranke a Ajingi; Kofar Gabas da Rimji a Bagwai; Sarkin Kogi da Rugar Bala a Bebeji; Muraye da Wabi a Bichi; Gorau da Wailare a Bunkure; Karas da Nasarawa a Dawakin Tofa; Kanwari da Tsugudida a Gabasawa; Gidan Masaka da Wangara a Kabo; Hayin Diga da Mayola a Kiru; Zide da Janbaba a Kunchi/Ghari; Gargaji da Ruku a Kura; Kaguwa da Rafin Gora a Madobi; Gulu da Bakin Kogi a Rimin Gado; Jali da Jakura a Sumaila; Tudun Makama da Gunsu a Takai; Gudda da Fanshata a Tofa; tare da wasu al’umma da dama a sauran ƙananan hukumomin da aka ambata.
Ya ce Waɗannan yankuna na buƙatar ci gaba da wayar da kai, shirye-shiryen kariya, da bin umarnin gargaɗin ambaliya a daminar bana.
Domin fuskantar haɗurran da ake hasashe, NEMA ta samar da Tsarin Gudanar da Haɗurran Sauyin Yanayi, Shirye-shirye da Rage Illoli na shekarar 2026
A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Dahiru Muhammad Hashim ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta amince da matakan rage ambaliya da suka hada da gina sabbin magudanar Ruwa da yashesu da sauransu.
A bangarensa sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano (SEMA) Isyaku Abdullahi Kubarachi ya ce za su ci gaba da shiga lungu da sako domin wayar da kai ga al’umma da suka hada da shugabannin gargajiya, kungiyoyin al’umma domin daukar matan kariya daga ambaliyar ruwa a damuranar bana.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su himmatu wajen yashe magudanar Ruwa tare tsaftace muhallansu.
Taron masu ruwa da tsaki ya gudana a Coronation Hall dake gidan gwamnatin Kano, ya samu halartar ma’aikatu da hukumomi daban daban da suka haɗa da lafiya, Karota, hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura, jami’an ƴan sanda, Sojoji, hukumar kashe gobara, da ƙungiya bada aji ta Red Cross, shugabannin gargajiya da sauransu.
