
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ranar Talata, 10 ga Nuwamba.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Abdulfattah bin Sulaiman Mashat, ya sanya hannu a madadin kasarsa.
Yarjejeniyar ta kunshi batutuwan rabon guraben aikin Hajji, masauki, sufuri, kula da lafiyar alhazai da kuma bin ka’idojin gwamnatin Saudiyya.
Hukumar ta ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen inganta ayyukan da ake yi wa maniyyata da kuma kare lafiyarsu yayin gudanar da ibadar.
A yayin taron, jami’in Saudiyya ya bayyana cewa an samu kashi 93 cikin 100 na gamsuwar alhazai da ayyukan Hajjin shekarar 2026, tare da yaba wa Najeriya kan bin wa’adin shirye-shiryen Hajjin.
NAHCON ta ce za ta hada kai da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da masu gudanar da aikin Hajji domin tabbatar da an kammala shirye-shiryen lokacin da ya dace.
