Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kasha 95 na ‘yanbindigar da ke addabar Kano daga jihar Katsina suke shigowa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai kananan hukumon Tsanyawa da Shanono domin jajanta musu da kuma halin matsalar tsaron da ya addabi yankin.
“Gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ake ganin suna fama da matsalar tsaro, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na dakile hare-haren ‘yan bindiga da kuma dawo da zaman lafiya.
“Gwamnatinmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa kowane yanki na jihar ya sami cikakkiyar kariya”. In ji gwamnan.
Haka kuma ya umarci jami’an tsaro da su ci gaba da su mayar da hankali, su kuma kasance masu saka idanu, tare da ƙara inganta tattara bayanan sirri cikin haɗin kai da al’umma.
