Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya da ta tsare na tsawon kwanaki 10, biyo bayan tattaunawar diflomasiyya da gwamnatin Najeriya ta gudanar, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta tabbatar.
Sakin sojojin ya biyo bayan wata ganawa da tawagar gwamnatin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta yi da shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a ranar Laraba.
A cewar ma’aikatar, gwamnatin Najeriya ta gabatar da neman afuwa a hukumance kan keta sararin samaniyar Burkina Faso, lamarin da ya haddasa tsare sojojin tare da jirginsu.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya tabbatar wa jaridar Punch cewa an kammala sakin sojojin Najeriya da aka tsare.
Sai dai har yanzu ba a bayyana takamaiman lokacin da sojojin za su dawo gida Najeriya ba, domin a cewar jami’ai, shirye-shiryen komawarsu na nan ana ci gaba da kammalawa.
