Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta kai agajin gaggagwa Karamar Hukumar Rano.
Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Rano Ibrahim Muhammad Malami ya bukaci hakan yayin gabatar da kudurinsa a gaban majalisar a ranar Talata.
Majalisar ta ce, gwamna ya umarci kwamishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusif ya gaggauta kai daukin gaggawa mazabun Rurum tsohuwa da Rurum sabuwa dake Karamar hukumar Rano domin dakile cutar da ta bulla a yankin. Da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 5.
“Kawo yanzu cutar a iya mazabu biyu na karamar hukumar kawai aka samu barkewar ta, sai dai akwai bukatar daukar matakin gaggawa domin shawo kan ta daga bazuwa ya zuwa wasu sassa”. In ji majalisar.
Majalisar ta kuma gargadi al’ummar birni da kauyukan Kano kan su kasance masu kai kawunan su ya zuwa asibiti domin daukar matakin gaggawa da zarar sun ji wani sabon sauyi a tattare da lafiyarsu domin gujewa yaduwar cuta har ta kai matakin da ba za’a iya shawo kan ta ba.
Wakilinmu a majalisar ya rawaito cewa, kudurin na Malamai ya samu cikakken goyon baya daga mambobin majalisar, inda suka bukaci bangaren zartarwa da ya dauki matakin da ya dace akan lokaci.
