Daya daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasa ya musanta zargin da wasu tsaffin sojojij suka yi a fififta manyan hafsoshin da aka yiwa ritaya kwanan nan na irin garar sallamar da aka shirya musu.
Babban Mataimaki na Musamman, wajen Watsa Labarai Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyan haka a hirarsa da BBC.
“Wannan sallama da ake magana a kan ta ba sabon abu bane domin kusan shekara guda ke nan da shugaban kasa ya amince da bayar da irin wannan hakki ga manyan hafsoshi”, in ji shi.
Wasu tsofaffin sojoji sun koka kan abin da suka kira gata da alfarma da ake nuna wa manyan hafsoshin sojin kasa da aka sauke kwanan nan.
Yayin da ƙananan jami’ai ke ci gaba da fama da rashin kula da kuma rashin biyan hakkokinsu duk da shekaru da suka kwashe suna hidimtawa kasa.
Tsohon Babban Hafsan Tsaro Christopher Musa, tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, kowannensu zai samu motar sulke daya mai daraja.
Sannan za’a dinga kulawa da ita, tare da maye gurbinta da sabuwa bayan duk shekara hudu, da kuma karin wata motar alfarma kirar Prado ko makamanciyar ta.
Wannan gata da aka nuna ma manyan sojojin da suka yi ritaya ya sanya tsoffin sojojin kokawa tare da ikirarin cewa ana nuna halin ko-in-kula da kuma bambanci a tsakanin manyan hafsoshin soji da ƙananan ta ɓangaren walwala da biyan hakkoki.
