Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan wani kuɗi da aka tura cikin ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya ce shi ko kwamitin yaƙin neman zaɓensa ba su nemi ko amince da kuɗin da aka tura da bayanin “Contribution Electioneering Campaign” ba.
Ya ce asusun bankin nasa na sirri ne, kuma ba kowa ne ya san bayanansa ba.
Don haka, ya ce abin mamaki ne yadda wasu suka samu bayanan asusun.
Ya kuma yi zargin cewa hakan na iya nuna an samu kutse cikin bayanan sirrin bankinsa.
Atiku ya yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki lamarin, yana mai gargadin cewa idan aka tabbatar da hakan, zai zama babbar barazana ga sirrin bayanan kuɗaɗen yan Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.
