Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta ƙaddamar da wata manhaja da za ta taimaka wajen gano wayoyin hannu da aka sace, tare da yaƙi da shigar da jabun wayoyi da waɗanda ba su cika ƙa’idojin da aka gindaya ba cikin kasuwar Najeriya.
Mai kula da ofishin hukumar shiyyar Kano, Injiniya Maigana Gidado, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Kano, inda ya ce manhajar za ta sauƙaƙa gano wayoyin da aka ƙwace daga hannun mutane da kuma mayar da su wajen mamallan su.
Maigana ya ce manhajar za ta baiwa masu amfani da waya da sauran waɗanda aka amince da su damar tantance sahihancin wayoyi masu amfani da katin SIM, domin tabbatar da cewa sun cika ƙa’idojin fasaha da hukumar ta tanada.
Gidado ya bayyana cewa hukumar ta samar da hanyar da za’a duba lambar IMEI ta waya domin tantance sahihancinta, inda ya buƙaci jama’a su riƙa bincika wayoyi kafin saye ta shafin yanar gizon hukumar,inda ya ce hukumar ta sauƙaƙa hanyoyin samun lasisi ga dillalan wayoyi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Maigana na jaddada cewa manhajar ba ta shiga bayanan sirrin masu amfani da waya, kamar saƙonni, hotuna, lambobin waya ko bayanan kuɗi, domin manufarta ita ce tantance na’urori da bin ƙa’idojin hukumar.
