Kwamitin da gwamnatin jihar Kebbi ta kafa don shirya bikin kamun kifin Argungu na bana, y ace suna fatan jawo masu zuba jari daga kasashen waje yayin bikin na bana, a matsayin wata dabarar ta bunkasa tattalin arzikin jihar.
Hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kebbi ta bayyana cewa masu zuba jari daga kasashen Turai da Asiya sun nuna matukar sha’awar halartar bikin na bana, inda ta bayyana ci gaban da aka samu a matsayin hadakar masu zuba jari da ke da alaka da al’adu da kuma yunkurin bunkasa su.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Talata, Babban Daraktan KIPA, Dokta Muhammad Kabir Kamba, ya ce gwamnatin jihar na yin amfani da wannan biki domin nuna dimbin albarkatun noma, ma’adinai da kiwo na Kebbi ga abokan huldar kasa da kasa.
A cewarsa, karuwar sha’awar masu zuba jari daga kasashen waje sakamako ne kai tsaye daga harkokin diflomasiyya da Gwamna Nasir Idris ya mayar da hankali kan zuba jari da kuma sauye-sauyen da ake yi na inganta harkokin kasuwanci a jihar.
An shirya gudanar da bikin kamun kifi da al’adu na kasa da kasa na Argungu na shekarar 2026 daga ranar 11 zuwa 14 ga Fabrairu,
