An ɗage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Ganduje da kuma wasu mutune shida.
Hakan ya biyo bayan da ɓangarorin da ke cikin shari’ar suka kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu.
Gwamnatin Jihar Kano ce ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci da haɗin baki wajen aikata laifi da karkatar da kuɗaɗen gwamnati na miliyoyin Naira.
A zaman kotun da aka gudanar a ranar Litinin, lauyan gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya bayyana cewa sun shirya gabatar da shaidu.
Amma lauyoyin masu kariya sun nemi ƙarin lokaci, suna mai cewa ba a mika musu wasu takardu na shari’ar ba, da suka ce suna da muhimmanci wajen kare tsohon gwamnan da matarsa.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta umarci dukkan ɓangarorin da su kammala miƙa dukkan takardunsu kafin zaman kotu na gaba.
Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba, 2025.
