An sassauta dokar hana zirga-zirga da aka kafa a garin Karim Lamido da sauran kauyuka fiye da goma a jihar Taraba, sakamakon wani rikici da ya barke kan batun mallakar wasu gonakin fadama.
Ana dai zargin rikicin ya yi sanadin asarar rayuka akalla ashirin, da gidaje da dukiyoyi masu dimbin yawa.
An sassauta dokar ce daga karfe shida na safe har zuwa karfe uku na rana, a maimakon dokar hana zirga-zirga dare da rana, wadda aka kafa ‘yan kwanakin da suka gabata, a wuraren da rikicin ya shafa a yankin karamar hukumar.
Wannan mataki ya biyo bayan lafawar da kurar tashin-tashinar da ta auku ne.
- Yajin aikin ma’aikatan NiMET Ya tsaida zirga-zirgan Jiragen sama a Najeriya
- ‘Ƴansandan bogi ɗauke da lodin tabar wiwi sun shiga hannu a Taraba
A cewar guda cikin dattawan an sassauta dokarce domin a bawa mutane damar su fita su nemi abinci da sauran kayan bukatun yau da kullum.
Kuma wannan rikici da ya haddasa sanya dokar, ya taso ne a tsakanin mutane makwabta wanda kuma suke zaune tare shekara da shekaru, sannan suna mu’amala sosai har ma akwai auratayya a tsakaninsu, to amma sakamakon batun mallakar fadama wanda saboda harkar noman ranai ya sa ta zama abar so da amfani sosai saboda za a iya samun kudi da ita to shi ne saboda kowa na son ya ga ya mallaki fadamar anan ne rikici ya balle.
