Wani rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa an sace wayoyin hannnu sama da miliyan 25 a shekara daya
Rahotan Hukumar na kididdigar ya nuna cewa hakan ya faru ne daga watan Maris na 2023 zuwa Afrilun wannan shekara 2024 mai karewa
Rahoton ya kuma ce mutane sama da mutum miliyan 17 ne suka rasa wayoyinsu a tsakanin wannan lokacin.
Hukumar ta kuma ce, an fi samun satar wayoyin ne a gidaje da kuma taron jama’a.
Sannan kashi 11.7 ne kacal na wadanda aka yi wa satar suka kai rahoton wurin ’yan sanda tare da neman taimakonsu.
Sannan rahoton ya kuma bayyana cewa ƙasa da kashi 10 na laifin satar wayoyi ne aka kai gaban ’yan sanda a bisa dalilai daban-daban.
sai dai wani abin mamaki shine kasa da kashi 21.4 na ’yan Najeriya ne, suke ganin hakan laifi ne da ya sabawa doka.
Duk da cewa satar waya na daga cikin manyan laifuka wanda kuma yaki cikin kundin aikata manyan laifuka inda yake da kashi 13.8. in ji rahoton.