Gwamnatin jihar ce ta bayar da umarnin rufewar sakamakon rikicin limanci da ta kai ga Limamai biyu suka dambace
Gwamnatin jihar Lagos ta rufe babban masallacin Juma’a na al’ummar Hausawa da ke Agege a jihar saboda rikicin shugabanci da Limanci.
Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi shine ya bada umarnin rufe masallacin nan take bayan da aka yi artabu kan wanda zai rika jan Sallah.
Rikicin Limancin ya samo asali ne bayan rasuwar babban limamin masallacin Sheikh Sharif Habib Abdul-Majid, a ranar Larabar makon jiya.
A wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga yadda masallata da Limamin masallacin suka kaure da fada har da doke doke.
Akwai bangarori uku da ke da’awar neman shugabancin masallacin, da suka hada da iyalan marigayin da ya rasu da magoya bayansa sai bangaren Na’ibi wato Mataimakin liman da yayi ikirarin cewa shine zai gaji buzun liman
Sai dai Karamar Hukumar Agege ta ce, ta rufe masallacin har sai abin da hali yayi dan gudun haifar da rikicin addini.
Shugaban karamar hukumar Ganiyu Kola ta ce, za su gayyaci kowanne bangare domin zama dasu anan gaba.