Gwamnatin jihar Kano ta gargadi magoya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da su guji yin kalaman cin mutunci ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tana mai cewa duk wanda ya aikata hakan zai fuskanci matakan ladabtarwa.
Daraktan yada Labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan yayin rabon babura ga magoya baya a gidan Gwamnatin Kano.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani rashin da’a ko cin mutunci ga Kwankwaso ba, inda ya bukaci magoya bayan gwamnan da su kasance masu nuna dattako, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar zazzafar muhawara sakamakon sabbin sauye-sauyen siyasa.
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara da martani biyo bayan ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP, lamarin da ya haifar da mabambantan ra’ayoyi a cikin Kwankwasiyya da al’ummar Jihar
