Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da tashinn wata gobara a babban asibitin karamar hukumar Rogo, wanda tayi sanadiyar konewar wure daban daban a asibitin.
Kakakin hukumar kashe gobara na Kano Saminu Yusuf Abdullahi shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya juma’a.
Ya kara da cewa, a binciken farko da hukumar ta fara gudanarwa ta gano cewa gobarar ta tashi ne sakamakon taratsatsin wuta da aka samu a babban asibitin karamar hukumar ta Rogo.
- Za a dauki sabbin ma’aikatan kashe gobara fiye da 200 a Kano
- Gobara: Gwamnan Kano ya bawa ‘yan kasuwar Kwalema tallafin naira miliyan 100
- Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano ya Ziyarci Kasuwar da aka yi gobara
Saminu Yusuf Abdullahi ya ce kawo zuwa wannan lokacin hukumar ta sake zurfafa bincike domin tattara dukkanin bayanan da ake da bukata kan musababin tashin gobarar.
Daga bisani Daraktan hukumar kashe gobara na jihar Kano Alhaji Sani Anas ta sake jan hankalin al’umma dasu ci gaba da kiyaye dukkanin wani abu da ka iya tashin gobara a koda yaushe.
