Shugaban kasar Amurka Donald Trump, yayi barazanar daukar matakin soji akan najeriya, matukar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, bata kawo karshen kisan kiyashin da yayi zargin ana yiwa Mabiya addinin kirista Najeriyar ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito shugaba Trump na bayyana hakan ne a Shafinsa na X, inda yace tuni ya umarci rundunar sojin Amurka da ta kasance cikin Shirin jiran umarnin sa game da mataki nag aba da zai dauka akan najeriyar.
A cikin sanarwar da ya fitar dai, shugaban yace Amurka zata dakatar da dukkan ayyukan jin kai da taimakon da take gudanarwa a najeriya nan take.
Jaridar Daily post ta rawaito cewar, Wannan dai na zuwa ne bayan da a juma’ar da ta gabata Shugaban na Amurka Trump ya zargi najeriya a matsayin kasar da ake yiwa Mabiya addinin na kirista kisan kiyashi,
To sai dai tuni Shugaban Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya suka musanta tare da yin watsi da zargin na Trump, lamarin da ya Sanya Trump din barazanar daukar matakin soji akan najeriya.
