Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Chika Malami da ke tsare hannun hukumar EFCC, ya zargi hukumar da hana shi damar cika sharuddan belinsa, kamar yadda ya bayyana sharuddan a matsayin masu tsauri da wuyar cikawa.
Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muhammed Bello Doka, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ikirarin da hukumar ta yi na cewa Malami ya ki amincewa da belinsa saboda har yanzu bai cika sharuddan belin da aka gindaya masa ba, yana mai cewa sharuddan wata dabara ce ta ci gaba da tsare shi saboda kawo manyan sakatarorin gwamnatin tarayya karkashin binciken gwamnati ba zai yiwu ba.
Dangane da zargin yunkurin kaucewa bincike, ya ce tsohon ministan shari’a mutum ne mai bin doka da oda, kuma bai taba yin yunkurin kaucewa bincike ba; don haka irin wadannan kalamai sun fito ne daga hukumar ba Malami ba.
Ya bukaci hukumar da ta kasance mai tsafta tare da gabatar da sharuddan belin da zai iya cikawa, da kuma daina amfani da kafafen yada labarai na cewa ya ki beli.
To sai dai hukumar ta musanta cvewa ta sanya siyasa cikin batun belin tana mai cewa ko yanzu tsohon ministan ta cika sharudan belin zasu bayar da shi.
