Ƙungiyar Dilallan Man Fetur ta kasa (IPMAN), ta cimma yarjejeniya da Matatar Dangote kan fara dakon man fetur kai-tsaye daga wurinsu.
Yarjejeniyar ta samu ne bayan makwanni ana tattauna wa tsakanin ɓangarorin biyu kan samar da man fetur a sauƙaƙe kuma a farashi mai rahusa.
Da yake magana da manema labarai a Abuja, shugaban IPMAN, Abubakar Garima, ya ce yarjejeniyar za ta inganta haɗin gwiwa tsakaninsu, wanda zai taimaka wajen samar da isasshen man fetur mai rahusa a faɗin ƙasar nan.
Garima, ya yi kira ga mambobin IPMAN da su bai wa matatar Dangote goyon baya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Ya kuma shawarci mambobin IPMAN da su dogar a da Matatar Dangote da matatun man Najeriya, wanda zai ƙara samar da ayyukan yi da kuma tallafawa manufofin ci gaba na Shugaba Bola Tinubu.
Tun da farko a watan Nuwamba, IPMAN ta bayyana cewa tsadar jigilar mai daga Matatar Dangote ta sa wasu dilallai neman mai rahusa ta hanyar shigowa da shi daga waje.